Sallah: Wata kungiyar a Bagwai ta tallafawa marayu da zawarawan yankin

Date:

Kungiyar tallafawa marayu da zawarawa da sauran marasa galihu ta garin Bagwai ta tallafawa marayu da Mata iyayen marayu da kayayyakin abinci da kudinsu ya kai Naira duba 250 domin gudanar da bukukuwan Sallah cikin annashuwa da jin dadi.

Da take jawabi wajen bayar ta tallafin kayayyakin abincin wanda ya gudana a fadar Dagacin Bagwai Sarkin Fulani Alhaji Aminu Adamu Bagwai, Sakatariyar Kungiyar Malama Wasila Sani Zakari wadda ta yi magana a madadin Shugabar Kungiyar, Malama Aishatu Inuwa Abubakar ta ce yara Marayu da iyayensu mata fiye da 200 ne suka amfana da wannan tallafin.

Hotunan Yadda Sarkin Kano ya gudanar da Hawan Sallah

Malama Wasila Sani Zakari ta ce wannan shine karo na biyu da Kungiyar take bayar da tallafi ga Marayu tun daga lokacin da aka kafa ta a shekaru uku da suka gabata.

Ta ce yanzu haka Kungiyar ta Sami damar yin rijista da sashin kungiyoyi na ma’aikatar ciniki da kasuwanci ta jihar Kano da hukumar yiwa Kamfanoni rijista ta kasa wato CAC.

Malama Wasila Sani Zakari ta kuma yi godiya ga duk wadanda suke taimakawa kungiyar don ganin an tallafi Marayun Musulunci daidai gwargwado sannan kuma ta bukaci sauran mawadata su bullo da tsare-tsaren tallafawa Marayu domin fita daga yanayin da muka sami kawunanmu na masifu daban daban.

Hajara Isma’ila Bagwai da Sarbiya Kabiru na daga cikin iyayen Marayun da suka amfana da tallafin inda suka bayyana jin dadinsu bisa tagomashin da Kungiyar ta yiwa yayansu a lokaci zuwa lokaci.

Daga cikin ayyukan da Kungiyar ke aiwatarwa sun hada da bayar da tallafin abinci da tufafi musamman a lokaci irin wannan na azumin Ramadan da kuma daukar nauyin karatun Marayu daga matakin Firamare zuwa Sakandare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...