Sallah: Ku Cigaba da Yiwa Nigeria addu’o’in Samun Cigaba – Minista Gwarzo

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’o’in samun ci gaba .

Ministan ya yi wannan kiran ne a cikin sakon sa na barka da sallah da murnar kammala azumin watan Ramadana lafiya .

A cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga karamin ministan Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24, yace ministan ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su amfani da darussan da suka koya a cikin watan Ramadana.

Hotunan Yadda Sarkin Kano ya gudanar da Hawan Sallah

Gwarzo ya shawarci ‘yan Najeriya da su kawar da duk wani bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su hada kai domin ciyar da Nigeria gaba. “Mu hada karfi da karfe domin marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya domin ya sake gina kasar nan.” Inji Ministan.

Ya nanata kudurin gwamnati mai ci a karkashin Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da ci gaba a fadin kasar nan.

Murtala Sule Garo Ya Yiwa Al’ummar Kano Barka da Sallah

Minista Gwarzo ya yi amfani da wannan dama wajen nanata kudurin ma’aikatarsa na ganin ta bi “Ajandar Sabunta Fata” ta Shugaba Tinubu domin samar da isassun gidaje masu inganci da araha ga ‘yan Najeriya.

Daga nan sai ya taya al’ummar musulmin duniya murnar kammala Azumin watan Ramadan da kuma da kuma barka da sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...