Yanzu-yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sabbin nade-nade a Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya amince da nada karin masu ba shi shawara na musamman da sauran shugabannin hukumomin gwamnati.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa jaridar kadaura24.

Yanzu-yanzu: CBN Ya Sake Karya Farashin Dala a Nigeria

Wadanda aka nada din su ne kamar haka:

1. Farfesa Ibrahim Magaji Barde, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattara kudaden shiga (IGR).

2. Dr. Abdulhamid Danladi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yan kano Mazauna kasashen waje II

3. Engr. Bello Muhammad Kiru, mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa.

4. Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) an sake nada shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.

5. Dr. Nura Jafar Shanono an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Daraktan hukumar (WRECA).

Kungiyar Yan Chanji Ta WAPA A Kano Ta Magantu Kan Karyewar Farashin Dala

6. Hon. Haka kuma Baba Abubakar Umar an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman zuwa babban sakataren gudanarwa, na hukumar kula da karantu masu zaman kansu da na sa kai.

7. Hon. Nasir Mansur Muhammad an nada shi Darakta Janar, Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs).

8. Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa zai zama mataimakin Manajan Darakta (DMD), Hukumar Noma da Raya Karkara ta Kano (KNARDA).

9. Engr. Mukhtar Yusuf, Mataimakin Manajin Darakta (DMD), hukumar WRECA.

Sanarwar tace nade-naden sun fara aiki ne nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...

Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya...