Daga Rahama Umar Kwaru
Tsohon Kwamishinan ma’aikatar karkara da cigaban al’umma a jihar Kano, Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci Gwamna Abba Yusuf da ya kyale Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, yana mai cewa bincikensa zai tona asirin uban gidansa na siyasar, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Kadaura24 a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Litinin, Dr. Musa Kwankwaso ya ce binciken ma yana da wata boyayyiyar manufa.
A cewarsa, bincikar gwamnatin Dr. Ganduje da ta shude wata kundunbala ce da zata iya bankado badakalar kudi da ake zargin ubangidan siyasar Gwamnan, Rabiu Kwankwaso, ya aikata a lokacin da yake gwamnan jihar.
Yanzu-yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sabbin nade-nade a Kano
Duk mun san cewa Dokta Rabiu Kwankwaso da Gwamna Yusuf na da burin sauya sheka zuwa APC, kuma kofar APC a bude take domin su shiga jam’iyyar ta mu.
“Amma ya kamata su dakatar da duk wadannan munanan manufofin da kuma neman bata sunan Dr. Ganduje, idan har suna son komawa jam’iyyar APC,” in ji tsohon kwamishinan.
Ya shawarci gwamna Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta raba kayan tallafin Abinchi masu yawa da gwamnatin shugaba Bola Tibubu ta baiwa jihar domin rabawa ga marasa galihu na jihar.
Yanzu-yanzu: CBN Ya Sake Karya Farashin Dala a Nigeria
Sai dai wani jigo a jam’iyyar NNPP a Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed, ya yi watsi da kalaman na tsohon kwamishinan, yana mai cewa abun da gwamnan Kano Abba Kabir yake kokarin yin na bincikar Ganduje bai sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba, kuma ba ruwan Kwankwaso akan maganar.
“Kada tsohon gwamna ya ji tsoron a bincike shi, idan ya san cewa yana da gaskiya ai bai Kamata ya rikice ba,” in ji Ahmed.
An sake samun sabon rikici tsakanin gwamna Yusuf da Ganduje bayan da gwamnan ya kaddamar da wasu kwamitocin guda biyu da za su binciki gwamnatin Ganduje na tsawon shekaru takwas.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kuma shigar da karar Ganduje, da matarsa, Hafsat, dansa, Umar, da wasu mutane biyar a gaban wata Kotu.