Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah karama.
Kadaura24 ta rawaito Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar, Aishetu Ndayako ya fitar ranar Lahadi.
Ministan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma lafiya.
Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi Sun Magantu Kan Labarin Rasuwarsa
Tunji-Ojo ya yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan dabi’u da halaye na kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, tausayi, irin na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.
Dan majalisar dokokin jihar kano Ibrahim kundila ya rasu
“Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da hadin kai domin ingantawa da samun zaman lafiya da hadin kai a kasar.
“Ministan na yiwa daukacin al’ummar musulmi barka da Sallah tare da addu’ar Allah ya karɓi ibadun da al’ummar musulmi suka yi a cikin watan na azumin Ramadan.