Daga Aliyu Danbala
Rundunar hadin gwiwa dake aikin samar da tsaro a karamar hukumar Gwarzo, Kano, ta dakatar da wani yunkuri da matasan unguwar Ruga dake karamar hukumar suka yi na kashe wasu mutane biyu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne.
Kadaura24 ta rawaito da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa da jami’an tsaron yankin, shugaban riko na karamar hukumar Gwarzo, Dokta Mani Tsoho wanda a bayyane ya kaduwa matuka game da yadda matasan suka fusata har suka lalata motocin jami’an tsaro, ya bukaci Matasa da al’ummar yankin da su kwantar da hankula tare da bayar da umarnin a kamo masu laifin cikin gaggawa.
Ramadan: Muhimman aiyuka 3 da ya Kamata mutane su rika a goman karshe -Khalifa Abdulganiyyu Getso
Dokta Mani Tsoho ya yi kira ga al’ummar yankin da su kasance masu bin doka da oda a nan gaba.
“Abin da ya dace a yi shi ne mika wadanda ake zargi da aikata laifuka ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Mani Tsoho.
A zantawarsa da manema labarai wani mazaunin garin Riga, mai suna Shugaba Sani Mato, yace wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutanen sun fito ne daga jihar Katsina kuma sun dade suna tayar da hankulanmu shi yasa yau muka far musu.
Limaman karamar hukumar Gwarzo sun koka da rashin biyansu alawu-alawus dinsu
Sani Mato ya ce garin na Riga dake mazabar Kutama yayi iyaka ne da jihar Katsina.
A Sanarwar da jami’in yada labarai na shiyyar Gwarzo Rabi’u Khalil ya aikowa kadaura24 yace, a nasa jawabin Hakimin Gwarzo Barde Kerarriyya Alh.Shehu Kabiru Bayero ya yabawa kokarin jami’an tsaro na dawo da zaman lafiya a cikin al’ummar da abin ya shafa.