Daga isah Ahmad Getso
Wani malamin Addinin Musulunci mai sunan Sheikh Khalifa Abdulganiyyu Ibrahim Getso ya bayyana wasu manya Ayyukan Alkhairi guda uku da ya kamata al’ummar musulmi yawaita yi a cikin wadannan Kwanaki goman karshe na watan Ramadan.
“Nana Aisha R,A tace manzon Allah (S A W) idan goman karshe na watan Ramadan yazo ya na shan damara, ya jajirce sannan ya tashi iyalansa ya kuma umartacesu da su dinga yin abubuwa guda 3 .
Ramadan: Karamar Hukumar Bichi ta Shirya Taron Shan Ruwa
1. Su yawaita Tsaiwar Dare
2. Su Dunga Yawaita Addu’a
3. Da kuma Yawaita karatun alqur’ani
Sannan Malamin ya kara da cewa akwai Daren lailatul wanda Allah yace yafi dare Dubu na sauran Watanni.
Malan ya kara da cewa a nemi daren a cikin goman karshe kuma a Kwanakin mara daren 21 da 23 da 25 da 27 da kuma daren 29 .
Rundunar yan sandan Kano ta kama wasu Yan Daba da Suka addabi unguwar Dorayi
Sannan ya Kara da cewa Akwai wani hadisi dagan hasanul basri yace manzon Allah S,A,W ya fada cewa idan watan azumi Ramandan ya zo Allah yana ‘yanta bayin Allah kullun mutun Dubu Dari Shida daga azabar Allah, Amma idan goman Karshe ta shigo ana maimaita adadin wadanda ake yantawa a baya a duk Rana Daya ana yanta mutun kimanin milyan 17 da Dubu dari 4 A kullun
Ya Kara da cewa mutane su tashi tsaye domin samun dacewa a wannan wata