Daga Rahama Umar Kwaru
Babbar kotun jahar Kano, ta yanke wa dan chinan nan mau FrankGeng Quarong hukuncin kisa ta Hanyar rataya har sai ya mutu.
Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji yanke masa hukuncin ne bayan tabbatar da hujjojin da Masu gabatar da Kara suka yi agaban kotun.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Tun a ranar 16 ga watan satumba 2022, Frank Geng, ya hallaka ummita a Unguwar jambulo dake jihar kano.