Da dumi-dumi: Kotu Ta Bayyana Shuruddan Bada Belin Murja Kunya

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Babbar kotun jihar Kano ta amince da bada belin shahararriyar yar Tiktok din nan suna Murja Ibrahim Kunya.

A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, Mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bada belin Murja Kunya a kan kudi N500,000 tare da kawo mutane biyu da za su tsaya mata .

Daya daga cikin wanda zai tsaya mata, dole ya zama makusancin Murja Kunya na biyu kuma dole ne ya kasance yana da kadara a cikin ikon kotun.

Dalilin Da Yasa ’Yan Sanda Suka Nemi Murja Kunya Ta Biya Su Diyyar Naira Dubu 500

Bayan haka, kotun ta umurci hukumar kula da asibitocin jihar Kano da kuma asibitin masu tabin hankali da su tabbatar da sallamar mai Murja bayan sun cika sharuddan belin.

Sannan Kotun ta haramtawa Murja Kunya yin wani rubutu ko bidiyon a dukkanin dandalin sada zumunta, har sai an kammala sauraren Shari’ar.

Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 16 ga Mayu, 2024 domin cigaba da sauraren karar .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...