NAHCON Ta Kara Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar alhazan, Farima Sanda Usara ta fitar a Yammacin wannan Lahadin.

Hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke son sauke farali a bana da su gaggauta cika kuɗin daga yanzu zuwa ƙarfe 11:59 na daren 28 ga Maris, 2024.

Hajiya Usara ta ce hukumar za ta rufe karɓar cikon kuɗin ne a ranar 29 ga watan Maris, kuma daga wannan lokaci babu wani maniyyaci da za su saurara matuƙar bai biya kuɗin kafin lokacin ba.

Hajjin Bana: Majalisar koli ta addinin musulunci a Najeriya ta nuna damuwa

A yanzu dai bayan wannan ƙarin, duk wani maniyyaci zai biya kusan Naira miliyan bakwai matuƙar yana son sauke farali a bana.

Idan za’a iya tuna cewa, tun a watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar alhazan ta ƙayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kuɗin kuejrar hajjin bana.

Ciyarwar Azumi: Shugaban Jam’iyyar APC ta Kano ta Caccaki Gwamnatin NNPP

Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar ƙara wa maniyyatan kuɗi a dalilin tsadar Dala da ke neman hana yi wa maniyyatan dawainiyar da aka saba yi musu ta masauki, abinci da makamantansu.

A wancan lokacin dai, NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudancin Najeriya su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan Arewa za su biya naira miliyan 4,699,000.

Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...