Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya musanta zargin cewa gwamnatin sa ta ware Naira Bilyan 6 domin ciyar da al’umma a watan azumin Ramadan, Inda ya ce Naira Biliyan ɗaya da Milyan ɗari da casa’in ne aka ware a matsayin kuɗin ciyarwar Azumin bana.
Gwamnan Yusuf ya bayyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a sahihin shafin sa na Facebook.
’Yan Bindiga Sun Saki Ɗaliban Kuriga
” Ina so na shaidawa duniya cewa, ainihin kuɗin da Gwamnatin mu zata kashe Naira Bilyan ɗaya da Miliyan Ɗari da casa’in da bakwai da dubu dari bakwai a gaba ɗaya kwanakin Azumin”. Acewar Abba Kabir Yusuf
ya ce ya lura da yadda a ‘yan kwanakin da suka gabata kafafen yaɗa labarai su kayi ta yaɗa cewa, gwamnatin kano ta ware Naira Bilyan 6 a matsayin kuɗin da zata kashe domin gudanar da shirin ciyarwar Azumin watan Ramadan.
Ya shawarci dukkan kafafen yaɗa labarai da su dinga tabbatar da kididdigar ayyukanmu ta hanyar tuntuɓar madogara mai tushe domin kaucewa faɗin abin da ba shine haƙiƙanin gaskiya ba.