Daga Shu’aibu Abdullahi Hayewa
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta kalubalanci gwamnatin NNPP da ta tabbatar da Naira biliyan 6 da ta kashe wajen ciyar da watan Ramadan na bana.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ne ya yi kalubalen yayin da ya kaddamar da rabon kayan tallafin azumi ga shugabannin jam’iyyar APC da magoya bayansa a Dawakin Kudu ranar Asabar.
Abdullahi Abbas, wanda ya bayyana shirin a matsayin abin kunya, ya bukaci gwamnatin jihar da ta nuna shaidar cewa ta kashe wadancan kudade wajen ciyar da abincin azumin Ramadan.
Ramadan :Dan Majalisa Dr. Ghali Ya Raba Kayan Abinchi, kuɗi 20m ga Al’ummar Mazabarsa
“Mun san cewa Gwamnatin Tarayya, Gidauniyar Bua da Dangote sun samar da kayan tallafin, don haka, su nuna mana shaidar cewa sun kashe kudaden da aka aka ware domin shirin ciyar ciyarwa “.
“Hatsin da muka rabawa magoya bayanmu an sayo su ne ta hanyar karo-karo da muka yi a junan mu duk da bamu da gwamnati,” in ji shi.
A cewarsa wadanda suka bayar da gudunmawar sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ministoci biyu na jihar, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas.
Gwamnan Kano ya bayyana ainahin kudaden da gwamnatin ta ware domin ciyarwar azumin
Sauran sun hada da: Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Dr. Nasiru Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule-Garo da shugaban ma’aikatan shugaban jam’iyyar APC na kasa Malam Muhammad Garba da Engr Abubakar Kabir Bichi.
Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce kayayyakin tallafin da za a raba sun hada da buhu 10 na manyan buhun shinkafa ga dukkanin mazabu guda 484 da buhunan gero.
Sai dai tuni gwamnatin jihar kano ta baki Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya musanta zargin cewa gwamnatin kano ta ware Naira Biliyan 6 domin ciyar da al’umma a watan azumin Ramadan.