Yadda Ake Bai Wa Waɗanda Ba Su Cancanta Ba Kwangiloli Na Miliyoyin Naira A Kano

Date:

Hukumar Kula da Tituna ta Kasa FERMA ta koka kan yadda wasu ‘yan kwangila da ba su cancanta ba ke samun kwangiloli na miliyoyin Naira a Jihar Kano.

Muƙaddashin Injiniyan da ke kula da tituna na tarayya a jihar, Ali Abdu ne ya koka kan lamarin yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Hukumar FERMA .

Ya ce, “Abin takaici, wasu ’yan kwangilar ba su da ƙwarewa, ba su da ma cebur ballantana kayan aiki amma suna samun kwangilar miliyoyin da za su aiwatar.”

Chushen 3.7: Dole Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria Ya Sauka Daga Mukaminsa

Ya ƙara da cewa wani ɓangare na matsalolin da hukumar ke fuskanta shi ne “rashin ababen hawa na masu aiki saboda waɗanda ake aikin fita sa ido da su ba sa aiki ko kuma suna buƙatar a canza su.

Injiniyan ya ƙara da cewa, titin gwamnatin tarayya da ke kan iyakokin Kano ya kai kilomita 990; yayin da akwai mai tsayin kilomita 423 ke da kyau, sai kuma mai tsayin kilomita 502 da ke da inganci matsaikaci 502 da kuma mai tsayin, kilomita 32 da ke cikin mummunan yanayi.

Kazalika, ya ce daga cikin kwangiloli guda 16 da aka ware a Kasafin Kuɗin 2023, an kammala shida kuma ana ci gaba da aikin biyar.

Sauyin Yanayi: Masu Sana’ar Kankara a Kano Sun Koka

Sai dai ya ce zuwa yanzu sun samu rahoton aikin wani dan kwangila ɗaya amma dai akwai ‘yan kwangila huɗu da ba su kai nasu rahoton ba.

Ali Abdu ya yi wa ‘yan majalisar bayanin kwangilolin da FERMA ta aiwatar a shekarar 2023.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Majalisar kan FERMA, Injiniya Aderemi Abasi Oseni, da sauran jiga-jigan ‘yan kwamitin sun tattauna da daraktocin shiyya da injiniyoyin kula da tituna na tarayya (FRME) daga shiyyar Arewa maso Yamma na ɗaya da na biyu na hukumar kan ayyukansu.

Shiyya ta ɗaya ta FERMA ta ƙunshi Kano, Kaduna da Katsina yayin da shiyya ta biyu ta haɗa da Zamfara, Sakkwato da Kebbi ƙarƙashin jagorancin Daraktocin shiyya ta biyu.

Injiniya Oseni ya ce, kwamitin ya himmatu wajen ci gaba da gudanar da ayyuka a karkashin kulawar ƙwararru.

“Mun zo nan ne don ganin yadda kuke gudanar da ayyuka.

“Za mu yi la’akari ne da ingancin abin da kuka gabatar da abin da muka gani a nan a zahiri.

“Ina tsammanin dangane da abin da muka gani za mu iya yabawa da ingancin ma’aikatan da muke da su a FERMA.

Daily trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...