Mun himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano – Gwamna Abba Kabir

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kudurinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Hukumomin tsaro na Kano a wani taron buda baki a gidan gwamnati da ke Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Litinin.

Yadda Gwamnatin Kano Ta Ci Gaba Da Rusau Duk Da Umarnin Kotu

A cikin sanarwar, gwamnan ya yabawa jami’an tsaro bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro da walwalar al’ummar jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta fara siyan kayan abinci domin rabawa ga al’umma, inda yace jami’an tsaro na cikin wadanda zasu amfana da tallafin.

Tinubu ya Sauyawa Lawan Jafaru Isa Mukami

Bugu da kari, ya yabawa gwamnatin tarayya musamman shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu bisa amincewa da rabon kayan abinci da za a yi ga marasa galihu a fadin jihar nan gaba kadan.

Gwamnan ya ja hankalin mahalarta taron da su ci gaba da rokon Allah Madaukakin Sarki da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da ma fadin Nijeriya a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Jami’an tsaro da dama ne suka halarci taron wadanda suka hada da Kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Hussaini Gumel da Birgediya Janar M.A Sadiq Kwamandan Sojojin Najeriya da ke Barikin Bukavu da Kwamandan J.K Adedeji na Kwalejin Kula da Kayayyakin Sojoji da ke Dawakin Tofa sun bayyana jin dadinsu da wannan tallafin. Gwamnatin jihar Kano za ta baiwa hukumomin tsaro.

Sun kuma jaddada aniyarsu ta tabbatar da tsaro a jihar Kano, inda suka bayyana taron buda baki a matsayin dandalin tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi inganta ayyukan hukumomin tsaro a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...