Daga Halima Musa Sabaru
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin shugabannin hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya zabi Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa (mai ritaya) ya zama shugaban hukumar gudanarwar hukumar, yayin da Dr Idris Muhammad Sani zai zama babban sakataren zartarwa na hukumar
Ja’afar Isa shugaba ya taba rike mukamin gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna daga 1993 zuwa 1996.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da masharci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Tashe: Rundunar yan sandan Kano ta bayyana shirin ta na yakar masu tada hankali
Dr Muhammad Sani yana da digiri na biyu da na uku a fannin ilimin addinin Musulunci. Ya kasance a lokuta daban-daban a matsayin Darakta-Janar na Makarantar Al-Iman Lafia, ya kuma taba zama Kwamishinan Ilimi jihar Yobe da dai sauransu.
ShugabaTinubu ya ce, yana sa ran sabbin shugabannin da aka nada za su yi amfani da gogewarsu wajen gudanar da hukumar, domin tabbatar da cewa gwamnatinsa na kokarin ilimantar da yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya da Almajirai don inganta rayuwar su .