Daga Ibrahim Husaini Dorayi
Dangane da yadda wasu matasa a jihar Kano ke ci gaba aikata miyagun laifuka ta hanyar amfani da al’adun gargajiya a lokacin azumin watan Ramadan, rundunar ‘yan sanda a jihar ta dauki kwararan matakan tsaro domin tunkarar duk wani mutum ko kungiyar da ke shirin yin amfani da wannan al’adar a bana domin aikata wani laifi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya ce an yi nazari sosai kan yadda ake aikata laifuka a jihar, kuma an gano cewa wasu matasa na shirin yin amfani da al’adar “Tashe” don haifar da rashin tsaro a jihar .
Gumel ya ce, “Watani uku da suka gabata mun gano wasu matasa da suke shirin yin fadan daba, domin su far wa mutane, su kwace musu dukiyoyinsu da sunan tashe”.
Shaguna sama da 100 sun ƙone a gobarar babbar kasuwar Sokoto
Ya ce saboda haka ne rundunar ‘yan sandan jihar ta dauki kwararan matakan tsaro domin magance kalubalen da ake fuskanta da kuma wanzar da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.
Gumel ya kara da cewa, an umurci dukkan manyan turawan jami’an ‘yan sanda (DPOs), da su tashi tsaye domin dakile duk wani yunkuri na ta da hankalin mutane yayin tashe a jihar kano .
Abba Gida-Gida ya Saukewa Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kano Kabakin Arziki
“Bugu da kari, rundunar ‘yan sanda ta kara sanya ido da kuma sintiri a wuraren da aka gano inda matasa ke should shirin yin amfani da al’adar Tashe wajen tayar da hankalin al’umma”.
Kwamishinan ‘yan sandan ya yi nuni da cewa, sassan sashin leken asiri na rundunar sun kara zage damtse don tunkarar barazanar tsaro da ke kunno kai.
Ya kara da cewa “Wadannan hanyoyin da za a bi don baiwa rundunar ‘yan sanda damar daukar matakin da ya dace da gaggawa ga duk alamun gargadin yiwuwar rashin tsaro da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin da kuma bayan lokacin Ramadan,” in ji shi.
Rundunar ‘yan sanda ta gayyaci wasu shugabannin al’umma, da suka hada da Malaman addini, da kuma shugabannin matasa masu domin tattaunawa da su kan yadda za a shawo kan matsalar musamman matasan da ke amfani da tashe wajen aikata laifuka maimakon bunkasa al’adar ta Tashe.