Dangote na ciyar da mutane Dubu Goma a Kano Kullum a watan Ramadan, Ya raba buhunan shinkafa Miliyan 1 a Nigeria

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyar Aliko Dangote, yana rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmi A kullum kimanin dubu Goma 10,000 a mahaifarsa jihar Kano

Gidauniyar ta kara fadada wannan taimakon ne ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan daya da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 13 a fadin jihohin kasar nan 36 da Abuja, da nufin rage mawuyacin halin da ake ciki a kasar nan sakamakon kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin Yanzu.

Wannan shirin na nufin rage wahalhalun da miliyoyin ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Bugu da kari, rabon ya haɗa da burodi kimanin dubu 20,000 a kullum ga mazauna Kano da Dubu 15,000 a kullum ga mazauna Legas, shirin ciyar da abincin an fara tun Shekarar 2020 yayin barkewar cutar ta COVID-19.

Tashe: Rundunar yan sandan Kano ta bayyana shirin ta na yakar masu tada hankali

Abincin da ake dafawa na Ramadan kyauta Ya ƙunshi jollof rice, Farar Shinkafa da stew, jollof spaghetti, kunu, wake, Tare da kaza da naman sa, da abin sha Ga kowane mutum.

Ana raba waɗannan abinci ne a masallatan Juma’a da tituna da Gidajen yari da gidajen marayu da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.

Wani da yaci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako mazaunin Garin Tarauni ya nuna jin dadinsa da wannan karimcin inda yace hakan ya taimaka masa wajen buda baki cikin sauki.

“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, Wannan abincin zai yi matuƙar taimaka wa Talakawa irina su sami wani abu da za mu yi buda baki dashi.

“Na san mutane da yawa a jihar nan waɗanda suke iya buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan abincin ya kawo sauki,” in ji shi.

Da take nuna jin dadin ta, Hajiya Inna Tukur, wacce taci gajiyar Tallafin, ta jaddada muhimmancin rabon abincin da Gidauniyar Aliko Dangote tayi, Musamman a wannan lokaci da ake cikin mawuyacin hali.

“A wannan mawuyacin lokaci da muke fama da cin abinci ko da sau biyu ko sau ɗaya a rana, karɓar irin wannan abinci mai dadi kyauta abu ne mai ban mamaki.

“Bani da komai sai Godiya gare ku da Aliko Dangote, ina rokon Allah Ya kara muku albarka,” inji ta.

Abba Gida-Gida ya Saukewa Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kano Kabakin Arziki

Baya ga rabon biredi kyauta da aka shafe shekaru huɗu ana yi, an shafe sama da Shekaru 30 ana ciyar da mabukata a Kano.

Ana Gudanar da wannan shiri ne daga gidan mahaifiyarsa dake unguwar Koki A jihar Kano da wuraren dafa abinci daban-daban. Shirin ciyarwar ya shafi mazauna Kano 10,000 a kullum tare da karin kumallo, abincin rana, da kuma abincin dare, wannan gagarumin taimakon ya ɗauki sama da Shekaru Talatin ana Gudanar dashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...