Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya raba kayan abinchi ga daukacin ma’aikatan dake aiki a gidan gwamnatin jihar, a wani bangare na tallafin watan azumin Ramadan.
Kadaura24 ta rawaito cewa kowanne ma’aikaci ya rabauta da babban buhun shinkafa 50kg da katan din makaroni da gero kwano 10 da kuma kudi Naira dubu 10 na cefane.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Shahararren Mawakin Hip Hop Ya Karɓi Musulunci A Amurka
Da yake kaddamar da shirin bada tallafin, gwamna Abba Kabir Yusuf yace ya basu tallafin ne domin su gudanar da ibadu watan azumin ramadan cikin nutsuwa tare da iyalansu.
” Kuna da matukar muhimmaci a wajen tafiyar da harkokin gudanarwa na gwamnati , don haka ya kamata kuma mu kyautata muku don ku ji dadin cigaba da ibadar azumin watan Ramadana”. A cewar Abba Kabir Yusuf
Umarnin Shigo da Kayan Abinchi shi Yan Nigeria Suke Bukata – Waiya ya fadawa Tinubu
Gwamnan yace bayan ga ma’aikatan gidan gwamnatin jihar kano suma sauran al’ummar jihar kano zasu amfana da tallafin kayan abinchi a cikin wannan wata, Mun samar da tallafin kayan abinchi ne domin saukakawa al’umma saboda mawuyacin halin da mutane suke ciki.
Wasu daga cikin ma’aikatan gidan gwamnatin da jaridar kadaura24 ta zanta da su sun baiwa jindadinsu da kabakin alkhairin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke musu a wannan wata mai albarka.
Sun kuma ce tallafin zai kara musu kwarin gwiwar cigaba da gudanar da aiyukansu kamar yadda ya kamata ba tare da gajiyawa ba.