Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Hasken Kan Umarnin Bude Bodar Nigeria da Nijar

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Fadar shugaban kasa ta ce umarnin bude iyakokin Nigeria da jamhoriyar Nijar da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar, ba wai yana nufin bada damar shigo da kayan masarufi da sauran kayayyakin da tsohuwar gwamnatin Buhari ta hana shigo da su kasar ba ne.

” Wannan umarnin yana magana ne kawai akan abubunwan da suka faru ko matakan da ECOWAS ta dauka na sanyawa ƙasar Nijar takunkumi sakamakon Juyin mulki da sojojin kasar suka yi, don haka umarnin shugaban kasar yana magana ne kawai a koma Inda ake a bara “.

Babban Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana hakan, yayin da yake yiwa kadaura24 karin haske dangane da umarnin da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar na bude iyakokin Nigeria da jamhoriyar Nijar.

Matar Shugaba Tinubu ta bayyana dalilin da suka sa bata tsoron mutuwa

Yace umarnin ba wai yana nufin a cigaba da shigo da kayan masarufi da sauransu ba ne, “dokokin mu na cikin gida na hukumar kwastam suna nan kuma jami’an hukumar zasu cigaba sa sanya idanu akan duk kayan da za’a Shigo da su Nigeria.

” Kamar yadda aka sani a dokokin hukumar Kwastam akwai kayan da aka aminta da su akwai kuma wadanda ba’a aminta a shigo da su ba, don haka dokar da aka sa a baya tana nan tana aiki musamman akan shinkafa da wasu sauran abubuwan amfani na yau da kullum har yanzu dokar tana nan tana aiki aka su”.

Ramadan: Zamu Kashe Naira Miliyan 15 Wajen Ciyar da Masu Karamin Karfi – Kantoman Dawakin Tofa

Idan za’a iya tunawa tsohon shugaban kasar Nigeria Muhammad Buhari shi ne ya rufe iyakokin kasar inda aka hana shigo da Shinkafa, kayan masarufi da sauransu da nufin inganta wadanda ake samar wa a cikin gida Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...