Daga Rukayya Abdullahi Maida
Karamin ministan gidaje da raya birane na Nigeria Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya yi kira ga al’ummar Musulmin Nigeria da su dage da rokon Allah ya magance matsalolin da suka dabaibaye Kasar .
Ministan ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na taya Musulmi Murnar zagayowar azumin watan Ramadan, wadda mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Cushe: Hatsaniya ta kaure a Majalisar Dattawan Nigeria
A cewarsa, “watan Ramadan daya ne daga cikin lokuta masu alfarma a Musulunci inda al’ummar Musulmi a fadin duniya suke gudanar da ibadu domin neman yardar Allah Subhanahu wata’ala, don ya ce yiwa Nigeria addu’a a wannan lokaci yana da matukar muhimmaci.
Zamu fi Baiwa Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Al’ummar Gwarzo Fifiko – Kantoman Gwarzo
Ya kuma yi kira ga daukacin musulman Nijeriya da su yi amfani da wannan damar wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya, ingantuwar tattalin arziki da kuma ci gaban kasa.
Minista Gwarzo ya kuma yi kira ga Limamai da Malamai da su yi amfani da wuraren wa’azi da tafsirinsu don sanar da al’umma muhimmancin zaman lafiya da hadin kai a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Ramadan: Dan Majalisar Bichi ya kaddamar da rabon Abinchin da ba’a taba yin irinsa ba a Kano
Ministan, yayin da yake bayyana damuwarsa kan halin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmad Tinubu wajen marawa manufofin gwamnatin bayan don warware matsalolin da Kasar take ciki.
Minista Gwarzo, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Azumin watan Ramadan domin neman taimakon Allah a kan kalubalen da kasar ke fuskanta.