Matsalar Tsaro: Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Baiwa Manyan Jami’an Rundunar Umarni

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Hussaini Gumel, ya umurci kwamandojin shiyya da Turawan ‘yan sanda (DPOs) dake jihar da su kara kaimi tare da samar da jami’an sintiri a dukkan makarantun firamare da sakandare, da dukkan manyan makarantun jihar.

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Sanarwar ta ce matakin ya yi daidai da umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun don tabbatar da tsaron makarantun da ke karkashin shirin Safe Schools.

Ramadan: Bayan Hisbah ta Kano Ta Kama Su, Wasu Matasa Sun Bayyana Dalilansu Na Kin Yin Azumi

Ya ce wannan umarnin ya shafi inganta tsaron rayuka da dukiyoyi, musamman tsaron makarantu da dalibai.

“An dauki matakin ne da nufin tabbatar da tsaro da tsaron dalibai, malamai, da ma’aikata da kuma bunkasa fannin ilimi gaba daya a jihar.

Ramadan: Ku yiwa Nigeria addu’i don ta fita daga mawuyacin halin da take ciki – Minista ATM Gwarzo

“Manufar kara yawan jami’an ‘yan sanda a wadannan yankuna shi ne don kara dakile ayyukan miyagun laifuka da samar da ingantaccen yanayi domin baiwa malamai da dalibai damar samun kyakykyawan yanayin koyo da koyarwa ba tare da fargaba ba.

“Saboda haka, Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci jama’a, musamman masu kula da makarantu, malamai, iyaye, da dalibai, da su baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro cikakken hadin kai tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi cikin gaggawa domin mu hada kai tare wajen samar da tsaro,” inji shi.

Ya bukaci jama’a da su ci gaba da kai rahoton duk wani motsin mutane ko wani abu da suka ji wanda basu yarda da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...