Cikin kararrakin fyade Dubu a Kano 15 kawai ake iya gurfanarwa a gaban kotu – NAWOJ

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ) reshen jihar Kano, Kwamared Hafsat Sani Ismail ta ce cikin kararrakin fyade 1000 da cibiyar wakata dake Kano take samu duk shekara guda 15 kawai ake iya gurfanarwa a gaban kotu.

Hafsat ta bayyana hakan ne a wajen wani horon da aka shiryawa yan jaridu kan kare hakkin dan adam da Cin zarafin al’umma da aka gudanar a Kano.

Ta ce, a cewar cibiyar WARAKA dake be bibiyar harkokin cin zarafin al’umma musamman mata da kananan yara asibitin musamman na Murtala Muhammad Kano, suna samun akalla wadanda aka yiwa fyade su dubu daya duk shekara, amma dari biyar ne kawai ake kai rahoto ga ma’aikatar shari’a, yayin da kusan 15 kawai ake iya kaiwa gaban Kotu.

Ma’aikatar Lafiya ta bayyana wadanda suka fi kamuwa da cutar HIV tsakanin Maza da Mata

Hafsat ta bukaci iyaye da su kara taka tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani abu da ya shafi take hakkin dan Adam, ko cin zarafin ya’yan su ga hukumomin da abin ya shafa domin dakile wannan matsalar.

Shugabar ta bayyana kudurin NAWOJ na hada kai da masu ruwa da tsaki wajen dakile cin zarafin mata da kuma kare hakkin mata da kananan yara.

Babban jami’in gudanarwa kafar yada labarai ta Stallion Times, Alhaji Isiyaku Ahmed ya shawarci kafafen yada labarai da su rika wayar da kan al’umma kan illar cin zarafin al’umma da kuma take hakkin dan Adam.

Ya ce kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar bayar da rahotannin take hakkin dan adam da cin zarafin al’umma da kuma bin diddigin shari’o’in cin zarafin don tabbatar da adalci ga wadanda aka ci zarafin su.

Malam Daurawa ya bayyana sunayen wadanda suka Sulhunta su da Gwamnan Kano

Isiyaku ya yi nuni da cewa, makasudin shirya taron ba da horon shi ne don a sanar da mahalarta taron yadda zasu wayar da kan al’umma kan illar take hakkin dan adam da bada damar bai daya ga kowa da kuma cin zarafin al’umma.

“Muna fatan za mu yi aiki tare don inganta ‘yancin ɗan adam da Magance wariya a tsakanin al’umma”.

Farfesa Aisha Isma’il ta sashin koyar da kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero dake kano ta gabatar da makala Mai taken ‘Understanding Human Rights and Social Inclusion in the Media’, Inda ta bayyana ‘yancin mata a matsayin ‘yancin dan Adam.

Ta bayyana cewa kafofin yada labarai na iya yin tasiri sosai kan yadda ake fahimtar daidaiton jinsi da haɗin kai tsakanin al’umma, tattaunawa da magance matsalolin.

Wasu daga cikin mahalarta taron da suka zanta da Jaridar kadaura24 sun bayyana horon da cewa ya zo a dai-dai lokacin da ya dace.

Shahararriyar kafar yada labarai ta Stallion Times ce ta shirya wannan horon na kwana daya kan ‘yancin dan adam da Magance wariya da tallafin gidauniyar MacArthur .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...