Gwamnatin Tarayya ta bayyana nasarori data samu sakamakon cire tallafin man fetur a Nigeria

Date:

Daga Rabi’u Usman

 

A yayin da ake ta cece-kuce kan batun cire tallafin man fetur da kuma tasirinsa ga tattalin arzikin kasar, Gwamnatin tarayya ta nuna cewa matakin ya haifar da karuwar sama da dala biliyan 30 na zuba jari kai tsaye daga kasashen waje (FDI) a sassa daban-daban.

 

Da yake zantawa da manema labarai a Legas a karshen mako, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, Ya yi karin haske game da saka hannun jarin da ke kwarara cikin mahimman sassa kamar masana’antu, sadarwa, kiwon lafiya, da mai da iskar gas, wanda ke nuna alamar canjin gaske ga masu saka hannun jari.

Muhimmiyar Sanarwa Daga Rundunar Yan Sandan Jihar Kano

Mohammad Idris ya yi nuni da wani alkaluma mai karfafa gwiwa daga hukumar kididdiga ta kasa (NBS), wanda ke nuni da cewa an samu ci gaban kashi 3.46 cikin dari a tattalin arzikin Najeriya a kashi na uku na shekarar 2023, wanda ya zarce yadda ake tsammani da kuma kafa harsashin ci gaba mai dorewa.

A karon farko kamfanin Al-ihsan ya shirya bita ga masu son yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a Kano

Da yake karin haske kan kokarin da Gwamnati ke yi na rage tasirin cire tallafin, Idris ya jaddada kara yawan kudaden da ake ware wa kananan hukumomin, da baiwa Gwamnoni damar magance matsalolin kasafin kudi da kuma ba da fifikon muhimman ayyuka kamar biyan albashi.

Da yake maida jawabi kan batun daidaita albashin ma’aikata, Idris ya tabbatar wa ma’aikatan Gwamnati kudirin gwamnatin Tinubu na ganin sun inganta rayuwarsu, inda ya bayyana shirin aiwatar da shirin bayar da kyautar Naira 35,000 na wucin gadi ga dukkan ma’aikata nan da ranar 1 ga watan Oktoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...