Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tana sanar da daukacin al’umma cewa jami’an rundunar ‘yan sanda mai lamba 52 (PMF) Squadron Challawa Kano za su gudanar da atasayen harbi na kwanaki biyu a Hawan Kalibawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano. daga 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranakun Talata, 5th da Laraba 6th na Maris 2024.
Sulhu: Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Gana da Sheikh Daurawa
2. An shawarci jama’a musamman mazauna kauyukan Dambazau, Gangaren Dutse, Tumfafi, Kakurum da Dandalama na kananan hukumomin Dawakin Tofa da Ungogo da kewaye da su nisanci wurin, kuma kada su firgita da karar harbe-harben da zasu ji.
3. Kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa fahimtar juna, addu’o’i, goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar
.
Sanarwa daga
SP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA, ANIPR, MNISMA,
JAMI’IN HULDA DA JAMA’A, NA RUNDUNAR