Gwamna Buni Ya Sami Gagarumar Nasara a Bangaren Ilimi da Lafiya a Yobe – Baba Malam Wali

Date:

Daga Samira Hassan

 

Gwamnatin jihar yobe ta ce ta sami nasarori masu tarin yawa ta fuskar Ilimi saboda dokar ta baci da gwamna Mai Mala Buni ya sanya don inganta rayuwar al’ummar jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Baba Malam Wali ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da wakiliyar Kadaura24 a Ofishinsa dake Damaturu, jihar Yobe.

Yace gwamnatin ta sanya dokar ta baci a bangaren ilimi ne sakamakon yadda aka sami zaman lafiya a jihar, don haka aka ga cewa babu bangaren da ya jikkata sosai a wajen yan boko Haram kamar bangaren ilimi.

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Jihar Kano Ta Bada Sabon Umarni Ga Masarautun Jihar

“Bayan ya fahimci cigaban da aka samu ta fuskar tsaro, gwamna Mai Mala Buni ya kafa kwamiti karkashin jagorancin shugaban jami’ar Jihar Yobe, Sanna kuma cikin kankani lokaci suka ba da shawarwarin yadda za’a sake gina bangaren ilimi a jiha da yadda za’a horar da malamai da Bude makarantun da aka rufe saboda matsalar tsaro a baya”. Acewar Baba Malam Wali

” Babu Shakka mun cimma nasarori masu yawa saboda zuwa yanzu mun sami damar sake farfado da gine-ginen makarantun da Boko Haram suka lalata, sannan mun baiwa malamai da yawa horon yadda zasu gudanar da aikinsu, sannan kuma muna samar da kayan koyo da koyarwa ga dukkanin makarantun jihar”.

Da dumi-dumi Sheikh Daurawa Ya Bayyana Dalilan sa na Yin Murabus Daga Kwamandan Hisbah ta Kano

Yace an Bude makarantun manya da kananan makarantun sakandire a jihar, musamman makarantun mata saboda Ilimin ya’ya mata yana da matukar muhimmaci a gare su, hakan tasa suka bai da hankali sosai wajen bunkasa ilimin nasu.

Dangane da batun kiwon lafiya, Sakataren gwamnatin jihar yoben yace gwamnatin Mai Mala Buni ya taka gani wajen inganta fannin kula da lafiyar al’umma jihar baki daya.

” Tun a shekara ta 2015 da gwamnan Mai Mala Buni ya hau kan mulki ya sha alwashin samarwa da gyara asibitoci akalla a kowacce mazabu da ake da ita a jihar, Inda yace daga cikin mazabu 178 da ake da su a jihar yanzu haka an sami nasarar kammala gyara asibitocin sha ka tafi a mazabu 140 don inganta lafiya da rayuwar al’ummarsa, sauran 38 din ma yanzu haka ana aikinsu kuma za’a kammala gyaran su nan bada jimawa ba”.inji Malam Wali

Yace bayan wancan aiki, gwamnan yana baiwa makarantun da suke da alaka da kiwon lafiya kulawa ta musamman domin tabbatar da cewa an sami ma’aikatan lafiya masu kwarewa da sani makamar aiki.

” Yanzu haka gwamna Mai Mala Buni ya dauki nauyin dalibai akalla sama da 400 da aka turasu karo karatun kiwon lafiya a makarantu daban-daban a kasashe daban-daban a fadin Duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...