Yanzu-yanzu: CBN ya sanar da matakan dakile hauhawar farashin Dala a Nigeria

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Babban bankin Najeriya ya sanar da matakinsa na siyar da kudaden kasar waje da yawansu ya kai dala 20,000 ga duk dan kasuwar chanjin da ya cancancta a fadin kasar.

Kadaura24 ta rawaito wannan dai na zuwa ne shukaru biyu, bayan da dakataccen gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, ya dakatar da siyar da kudaden kasashen waje ga kamfanonin BDC masu na hada-hadar kudaden kasashen waje.

Babban bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sabuwar takardar da aka fitar, mai dauke da sa hannun daraktan sashen kasuwanci da musayar kudi, na bankin Hassan Mahmud, a ranar Talata.

Yan Sanda Sun Kama mutane 9 Masu Chanjin kudaden Waje ba Bisa ka’ida ba

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne da nufin gyara kura-kuran da ake samu a bangaren ‘yan kasuwar canji a Najeriya da kuma cike gibin da ake samu a kasuwar canjin a baya.

Ta ce za a rika sayarwa kamfanonin chanjin duk dala 1 akan Naira N1,301. wanda ke nuni da cewa an sami raguwar adadin kudaden da aka kashe a kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya mai cin gashin kanta .

Idan Muka Cigaba da Hakuri Al’ummar Nigeria Da Yawa ne Zasu Mutu – Shugaban Yan Kwadago

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan sauye-sauyen da ake samu a kasuwar canji, da nufin cimma daidaiton farashin canji na Naira a kasuwa, babban bankin Najeriya ya lura da yadda ake ci gaba da samun tabarbarewar farashin a kasuwar canji .

Don haka, CBN ya amince da siyar da kudaden kasashen waje ga kamfanonin da suka cancanta domin biyan bukatar hada-hadar da ba a ganuwa. Za a siyar da dala 20,000 ga kowane kamfanin BDC akan farashin N1,301 kowacce Dala daya, daga yau, 27 ga Fabrairu 2024 domin saisaita al’amura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...