Daga Ibrahim Abubakar Diso
Gwamnatin jihar Kano tace ta amince iyayen ‘ya’yan su ke makarantu a makarantun kwana a jihar da su ziyarci daliban a ranar Asabar 2 ga Maris, 2024.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan wayar dakan al’umma na ma’aikatar Ilimi ta jihar kano Balarabe Abdullahi kiru ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.
Yanzu-yanzu: CBN ya sanar da matakan dakile hauhawar farashin Dala a Nigeria
Sanarwar tace iyayen daliban zasu iya fara Ziyartar ya’yan nasu tun daga karfe 9:00 na safe zuwa 5:00 na yamma a ranar da aka sanya.
A cewar sanarwar an umurci iyayen daliban da su da su tabbatar da bin ka’idojin da suka shafi ziyarar.
Yan Sanda Sun Kama mutane 9 Masu Chanjin kudaden Waje ba Bisa ka’ida ba
Sai dai sanarwar ta ruwaito kwamishinan ma’aikatar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana jin dadinsa da irin goyon baya da hadin kai da aka saba baiwa ma’aikatar tare da yi wa daliban da iyayensu fatan kammala ziyarar cikin nasara.