Yadda Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Aiwatar da Rahoton Oronsaye, Don Haɗe Wasu Hukumominta

Date:

Daga Hauwa Muhammad

 

Majalisar zartaswa ta Nigeria (FEC) ta amince da aiwatar da wani bangare na rahoton Stephen Oronsaye Panel don hade wasu hukumomi, ma’aikatu, da wasu kwamitoci, yayin da wasu za a rushe su wasu kuma a chanza musu matsugunni.

An yanke wannan shawarar ne a taron majalisar zartarwar ta kasar da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

A cewar mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin gudanarwa Hadiza Bala Usman, ta ce an dauki matakin ne domin rage kashe kudade kan harkokin mulki da kuma daidaita yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.

Majalisar ta kuma karbi rahoto daga kwamitin ma’aikatun da aka kafa domin duba al’amuran shirin zuba jari na kasa.

Majalisar ta kuma amince da fara biyan kudi kai tsaye ga gidaje miliyan 12 da suka kunshi ‘yan Najeriya miliyan 60 tare da wasu muhimman tsare-tsare.

A shekarar 2011, shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin tsarin mulki da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya inda Oronsaye ya zama shugaban kwamitin.

A ranar 16 ga Afrilu, 2012, kwamitin ya gabatar da wani rahoto mai shafuka 800 wanda ya gano, yadda aiyukan wasu hukumomin suke karo da juna wanda hakan yana haddasa almubazzaranci wajen kashe kudaden gwamnati.

Rahoton ya ce akwai ma’aikatu da hukumomi 541 inda ya bayar da shawarar cewa a rage 263 zuwa 161, a soke hukumomi 38 sannan a hade guda 52.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...