Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar yan sandan Nigeria ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin bai wa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar kariya, sai dai ta ce za ta ɗauki duk wasu matakan hana ɓarkewar rikici a yayin zanga-zangar.
” Zamu ajiye jami’an mu a ko ina a fadin Nigeria cikin shirin ko ta kwana domin tabbatar da masu zanga-zangar basu karya doka da oda ba”
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, da ta fitar kwanaɗaya kafin zanga-zangar tsadar rayuwa da ƙungiyar ƙwadago ta Nigeria ta kira a faɗin ƙasar.
Cikakken Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Haramtawa Ado Gwanja Yin Waƙa, Bayan Kama Shi
A cikin sanarwar wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar ƴansandar ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce “Rundunar ƴansanda na sane da ƴancin da al’umma ke da shi na yin zanga-zanga cikin lumana kamar yadda doka ta tanada.”
Zargin Juyin Mulki: Helkwatar tsaron Nigeria ta Magantu ta Batu
” Muna kira ga yan Nigeria da zasu gudanar da zanga-zangar da su tabbatar basu karya doka ba, yayin zanga-zangar, su yi ya cikin kwanciyar hankali da lumana” a
Sai dai rundunar ta ce “yayin da take martaba ƴancin yin zanga-zanga cikin lumana, rundunar ƴansandan ta Najeriya ta ce za ta sanya ido kan duk wanda ya shiga zanga-zangar da mummunar manufa.”
Sanarwa tace rundunar ta ce ba za ta ɓata lokaci ba wajen murƙushe su ta duk hanyar da ba ta saɓa wa doka ba.