Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Kungiyar siyasa da zamantakewar ta al’ummar Yarabawa, (Afenifere), ta bukaci yan kabilar Yarbawa da su guji shiga duk wata zanga-zanga da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya yi a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu.
Tun da farko dai kungiyar NLC ta bayyana shirin shiga yajin aiki da zanga-zangar lumana na kwanaki biyu domin nuna rashin amincewa da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu sakamakon tashin gwauron zabi da kayan masarufi suka yi a sakamakon cire tallafin man fetur da faduwar Naira kyauta.
Tuni dai wasu fusatattun ‘yan Najeriya suka yi zanga-zanga a jihohin Neja da Oyo da Osun Kano da dai sauransu, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki kwararan matakai domin kawo karshen wannan kuncin.
ECOWAS ta Bayyana Dalilan da Suka sa Ta Janyewa Nijar, Mali da Burkina Faso Takunkumi
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, shugaban kungiyar ta Afenifere, Reuben Fasoranti, ya bukaci ‘yan Najeriya da su fahimci hakikanin kalubalen da kasar ke fuskanta.
Ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu na kokarin warware matsalolin da ta gada a tsawon shekaru.
“A matsayina na shugaba mai kishin kasa, ina kira ga kowane dan kabilar Yarbawa namiji da mace, babba da yaro, da sauran ‘yan Nigeria baki daya, da su yi hakuri su guji shiga zanga-zanga ko ayyukan da ka iya tada zaune tsaye,” in ji shi.
“Kuncin rayuwa, yunwa, da hauhawar farashin ba abun bane mai dadi ba. Duk da haka, dole ne mu fahimci gaskiyar kalubalen da kasar mu take ciki, wanda gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke kokarin warwarewa.
“Yayin da muke la’akari da irin wahalhalun da jama’armu ke fuskanta, yana da kyau mu gane cewa wadannan matakan tattalin arziki, duk da cewa suna da wuyar gaske, suna daga cikin manyan tsare-tsare da nufin dawo da ci gaban tattalin arziki da kwanciyar hankali a Nijeriya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi hakuri da Kokarin da gwamnati mai ci take yi, inda ya yarda cewa tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu na da tsauri sosai .
EFCC ta Kama Mutane 11 bisa Zarginsu da Sayar da Sabbin Kuɗi a Kano
A cewar dattijon, ya kamata ‘yan Najeriya su amince da kudirin gwamnati na kyautata rayuwar ‘yan kasa.
“Yana da kyau a lura cewa cire tallafin man fetur da yawo da darajar Naira ba abu ne na wasa, domin duk mun san irin barnar da aka yi wa ci gaban kasarmu ta hanyar hada-hadar kudade ta hanyar da bata dace ba .