Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Marubucin Shirin nan mai dogon zango na Labarina Yakubu M Kumo ya bayyana cewa akwai bukatar Mutane musamman masu kallon fim din Labarina su san cewa fim suke kalla ba tatsuniyar gizo da Koki ba.
Ga masu bibiyar shirin fim din Labarina a wannan makon an nuna Inda jarumin shirin Sadiq Sani Sani ( Mainasara) ya gama baiwa jarumar fim din Fatima Husaini Abbas ( Maryam) labarin irin wahalhalun da ya fuskanta da dalilinsa na sauya kansa daga mai kudi zuwa talaka, Inda har ta amince ta aure.
Marubuci Yakubu M Kumo ya bayyana hakan ne sashin shafinsa na Facebook a ranar asabar.
Zanga-Zangar NLC: Kungiyar Yarbawa Ta Baiwa Yan Kabilar Umarni
“Mainasara yana gama ba da labari sai Maryam ta fashe da kuka ta durƙusa tana ba shi haƙuri. Daga nan su ka sasanta su ka koma gida aka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da annashuwa. Taƙurunƙus…🤔”.
Yakubu M Kumo yace “Wai haka kuke son labarin ya kasance kamar tatsuniyar gizo da ƙoƙi? Series fa kuke kallo, idan babu ‘conflict’ da ‘obstacle’ ai ba labari ke nan. Dole watarana sai wanda ya ke birge ku ya ba ku haushi, ko kuma wanda ya ke ba ku haushi ya birge ku”.
ECOWAS ta Bayyana Dalilan da Suka sa Ta Janyewa Nijar, Mali da Burkina Faso Takunkumi
Marubucin ya dai bayyana waɗannan kalamai ne a matsayin martani ga masu ganin baiken Maryam Saboda ta ki yadda da mijin nata bayan ta Gano mai kuɗi ne ba talaka ba kamar yadda ya bayyana kansa.
Tun bayan kallon Shirin a ranar Juma’at data gabata al’umma musamman matasa a dandalin sada zumunta suke ganin Maryam din bata kyauta ba, Inda wasu suke cewa bata da imani saboda ta kasa tausaya masa bayan kuma ya bata labaran duk wahalhalun da ya sha.
Watakila nan gaba kaɗan Jamila ce za ta zama abar yabo ba Maryam ba. Wa ya sani? 🤫