Iftila’i: Gobara ta Tashi a Gidan Karamar Ministar Abuja Mariya Bunkure

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

A ranar Lahadin nan gobara ta tashi a gidan karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, da ke Asokoro, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

Mukaddashin Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Babban Birnin Tarayya Abuja, Amiola Adebayo, ya tabbatar wa wakilin Majiyar kadaura24 faruwar lamarin.

Adebayo ya bayyana cewa gobarar ta kone bene na farko na ginin gaba daya.

Marubucin Fim din Labarina Ya yiwa yan kallo Martani game da Shirin na Wannan makon jiya

Ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:45 na safe, sai dai ya ce jami’an hukumar sun isa wurin ne ‘yan mintoci kadan bayan da suka samu kiran gaggawa daga gidan ministar.

“Dukkan su suna a kasan benen ba su san cewa wutar ta tashi ba, don haka basu sanar da hukumar kashe gobara akan lokaci ba. Duk da cewa sun ce sun kira layinmu bamu daga ba, amma dai mu kawai kiran gaggawa ne ya shigo mana”.

ECOWAS ta Bayyana Dalilan da Suka sa Ta Janyewa Nijar, Mali da Burkina Faso Takunkumi

“Da isa wurin, sai muka ga cewa bene na farko na ci wuta. Don haka abin da za mu iya yi shi ne kawai mu hana wuta yadawa zuwa sauran sassan gidan, da kuma gine-ginen da ke kusa. Da kuma tabbatar da cewa ba a rasa rayuka,” in ji shi.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba, ko da yake mai taimaka wa ministar harkokin yada labarai Austin Elemue shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...