Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin Arzikin kasa zagon kasa EFCC, sun kama wasu mutane 11 (11) da ake zarginsu da, sayar da sabbin takardun Naira don kasuwanci.
An kama su ne a ranar Litinin, 19 ga Fabrairu, 2024, biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu, inda suke rufe fuskokin suna sayar da sabbin takardun kuɗin a kan titin Legas, daura da babban bankin Najeriya, Kano.
ECOWAS ta Bayyana Dalilan da Suka sa Ta Janyewa Nijar, Mali da Burkina Faso Takunkumi
Su dai masu waccan sana’ar suna sayar da sabbin takardun kuɗin ne musamman ga wadanda suke biki ko wasu al’amura .
Wadanda ake zargin sun kware wajen sayar da takardun kudi na Naira. Don haka aka kama wasu mutane 5 a cikin masu sayar da sabbin takardun Naira ga jama’a.
An kuma kama wasu ma’aikatan banki guda shida da ake zargin suna sayar da takardar kudin Naira ga masu siyar da sabbin kuɗin.
Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.