Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Rahotanni da ga jihar Neja na baiyana cewa wasu ɓatagari sun tare tireloli makil da kayan abinci da kayan abinci a yankin Suleja, lamarin da ya sa sojoji suka yi harbi sama don korar su a yau Alhamis.
Wani ganau, Alhassan Abdullahi, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa ɓatagarin, wanda suka kona tayoyi sun tare tirelolin da ke tahowa daga Abuja zuwa Kaduna.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta Dauki Matakan Rage Tsadar Iskar Gas a Nigeria
Ya ce sun sace buhunan kayan abinci iri-iri, musamman shinkafa kafin sojoji su isa wurin.
Yadda kamfanonin Kirifto ta Haddasa Tashin Farashin Dala a Nigeria
“Allah Ya sanya sojoji sun isa wurin sannan suka fara harbin bindiga a iska don tsoratar da ɓatagarin. Amma ko da hakan, da yawa daga cikinsu sun tafi da buhunan shinkafa da katan-katan na taliya da sauran kayan abinci.”
Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da wahalhalun da kasar ke fama da shi wanda ya haifar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar.