Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Muhammad Buhari, ya karbi bakuncin shugabannin gidauniyar (Qatar Charity Foundation) ƙarkashin jagorancin Mr. Yousef Al-kuwari, a gidansa na Daura da ke jihar Katsina.
Katsina Reporters ta samu cewa, mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon. Faruk Joɓe, na daga cikin waɗanda suka tarbi shugaban gidauniyar, a ranar Laraba 21. ga watan Feb. 2024.
Kazalika, gidauniyar ta baiwa tsohon shugaban ƙasar Muhammad Buhari, kyautar sabuwar takobi tare da yi mashi murna kan yadda ya gama mulki lafiya.