Daga Isa Ahmad Getso
Tsohon dan takarar gwamnan jihar kano a tutar jam’iyyar PDP Alhaji Jafar Sani Bello ya bukaci gwamnatin Kano da ta gudanar da bincike kan yadda akai aka fitar da Murja Ibrahim kunya daga gidan gyaran hali.
” Wannan lamari ya taba kimar gwamnatin Kano, wadda a koda yaushe take ikirarin cewa ita ta daban ce, wadda ke kokarin dora komai akan tsari, ya kamata gwamna ya sa a binciko wadanda suke da hannu kuma a tabbatar an hukunta su don gudun kada wasu su sake aikata hakan a nan gaba”.
Jafar Sani Bello ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Jaridar kadaura24 a safiyar yau litinin.
Yace barin lamarin haka ba tare da daukar mataki zai zubar da kimar Kano da Shari’ar Musulunci, sannan kuma zai bada dama fitsararrun mutane da ke takamar uwa a gindin murhu su cigaba da cin karen su.
Batun ajiye aikin Sheikh Daurawa, Hisbah ta Magantu
” Da na karanta labaran da akai akan wannan lamarin, na damu sosai saboda yadda kalaman Mai Magana da yawun kotunan Musulunci na jihar Kano su ka dinga cin karo da juna da na hukumar kula da gidan gyaran hali”. A cewar Jafar Sani Bello
” Akwai abun mamaki ace an bada aron wanda ake tuhuma bayan alƙali ya bada umarnin tsare shi a gidan gyaran hali, amma wai ace an baiwa lauyoyin gwamnatin jihar Kano aron wanda ke tsare domin ya amsa wasu tambayoyi wannan ba maganar da hankali zai dauka bane, ashe masu gabatar da tuhuma dama ana basu aron wanda ake tuhuma bayan an ba da umarnin tsare shi?”.
Yace dama lauyoyin gwamnatin jihar Kano suna da wanna damar? Ca nake gidan yarin ya kamata su je suyi duk tambayoyi da zasu a karkashin kukawar ma’aikatan hukumar gyaran hali su tafi?
” Ya Kamata mai magana da yawun kotunan Shari’ar Musulunci na jihar Kano ya sani yana magana ne da akilan mutane, don haka akwai bukatar ya tantace mana shin belin ta aka bayar ko kuma aronta aka bayar? Tare da bayyana ma alumma ranar da alkali ya zauna ya bada umarnin bada belin ko aron tare da kuma lauyan da ya gabartar da bukatar hakan a cikin zauren kotu akai zaman ko a ofishin mai shari’a. Inji Jafar Sani Bello
Kotun da ke Shari’ar Murja Kunya ta Bayyana Dalilan Fitar da ita Daga Gidan Yari
Jafar Sani Bello yace ya kamata hukumar gidan gyran hali don su kubuta daga zargi hannu cikin lamarin su nunawa al’ummar jihar kano takardar da aka gabatar mu su na beli ko aro da kuma wacca alƙali ya amince a bada belinta ko aronta, ko kuma a fito da takardar da lauyoyin gwamnati suka bukaci a basu aro tuhumamme, sannan ya kamata a yiwa mutane bayani shin lauyoyin gwamnati ne suka gurfanar da ita koko hukumar Hisbah, in Hisbah ce ta gurfanar da ita me ya kawo lauyoyin gwamnati cikin maganar harda da ma karbar beli?
Yace akwai bukatar gwamnatin jihar Kano ta binciki lamarin sosai a kuma hukunta wadanda aka samu da hannu, don tabbatar da alumma cewar gwamnati ba zata lamunci yi wa sharia musamman ta musulunci karan tsaye ba.
Idan dai za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito ana ta ce-ce ku- ce akan yadda aka saki Murja Ibrahim kunya daga gidan yari bayan da Hukumar Hisbah ta jihar kano ta kamata tare da gurfanar da ita a gaban kotu.