Daga Hafsat Lawan Sheka
Hukumar kula da ingancin Abinchi da Magunguna ta kasa NAFDAC ta umarci kamfanonin dake hada magunguna da masu shigo da shi Nigeria da su dakatar da bayar da magunguna ga yan magani dake Kasuwar Sabon Gari a
Hukumar ta bayyana wannan umarni ne ta wata takardar da aka fitar a ranar Lahadi tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN).
An bayyana cewa, umarnin ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka ta yanke a ranar Juma’a, inda ta umarci dilolin magunguna da su gaggauta ficewa daga kasuwar Sabon Gari, su koma cibiyar hada-hadar sayar da kayayyaki da ke unguwar Dangwauro a Kano.
Iftila’i: Goodluck Jonathan ya Mika Kokon Bararsa ga Yan Nigeria
Da suke mayar da martani kan hukuncin, mambobin kungiyar dillalan magunguna ta Najeriya NAPPMED da ke Kasuwar Sabon Gari sun ce sun rufe shagunan su a ranar Asabar din da ta gabata tare da shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
Hukumomin biyu sun bayyana cewa an bayar da wannan umarni ne domin hana yaduwar magunguna marasa inganci da jabun magunguna a jihar Kano.
Hukuncin Kotu: Yan Kasuwar Magani a Kano Sun koka tare da daukar mataki
Takardar Umarnin mai taken, ‘Cikin gaggawa: An bukaci masu masana’antu da masu shigo da magunguna da su daina ba da magunguna ga yan magunguna dake titin Neja da Kasuwar Sabon Gari, Kano.
“Duk wani kamfanin da aka samu ya bijirewa wannan Umarnin hakan zai iya sawa ya yi asarar lasisin yin Magaji a Nigeria”.
“Yan kasuwa, asibitoci da sauran su ma su lura.”