Matsalar tsaro: Malam Shekarau ya baiwa Tinubu Shawara

Date:

Daga Hafsat Yusuf Abubakar

 

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa Najeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 200 ba ta da ‘yan sanda miliyan daya, yana mai nuni bada shawarar cewa ya kamata duk shekara a dauki ‘yan sanda kusan 50,000 domin magance matsalar tsaro data addabi wasu sassa na kasar.

Malam Shekarau, wanda tsohon Sanatan kano ta tsakiya ne ya bada shawarar yayi da ya tattauna da gidan talabijin Channels a cikin Shirin Politics Today a a ranar Alhamis.

Ya bayyana hakan ne a bisa la’akarin da gwamnatin tarayya da na jihohi suka yi na samar da ‘yan sandan jihohi domin magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Kotu A Kano Ta Yanke Wa Mutumin Da Aka Kama Da Murja Kunya Hukunci

Tsohon Ministan Ilimi ya ce, “(Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu) Buhari ya yi alkawarin daukar yan sanda 10,000 duk shekara, amma kwamitina na Majalisar Dattawa da ke kula da fensho ya gano daga asusun fansho na ‘yan sanda, a duk shekara, ‘yan sanda 5,000 ne ke barin aikin ko dai. ta hanyar mutuwa, ritaya ko wasu dalilai.

“Don haka idan za su dauki yan sanda 10,000 duk shekara kawai ku dauka za ku dauki 5,000 ne, kuma na gabatar wa da gwamnati takarda, ina da ita, inda na bayyana yadda za’a rika daukar yan sanda 50,000 da 60,000 ba tare tsayawa ba. ” in ji shi.

Da dumi-dumi: Hukumar Hisbah ta sake kama wata yar TIKTOK a Kano

Malam Shekarau ya ce babu yadda za a yi ‘yan sanda 300,000 su iya kare yan dukkanin yan Nijeriya baki daya saboda adadin bai isa ba.

Muhimmancin Masarautun Gargajiya ga Tsaro

Har ila yau, tsohon gwamnan ya ce kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya ba zai yi nasara ba idan ba a sanya sarakunan gargajiya a cikin aikin ba.

Shekarau ya ce sa idon al’umma da tattara bayanan sirri shi ne abu mafi muhimmanci idan gwamnati da gaske ta ke wajen dakile matsalar rashin tsaro.

” Abin da kawai muke cewa shi ne sa-ido a tsakanin al’umma, tattara bayanan sirri daga al’umma. Su wadannan ’yan taaddar ba a wata duniyar suke ba, suna zauna ne a cikin jama’a, abin da muke bukata shi ne gwamnati sanya al’umma a ciki.

“Kada ku manta ba za mu iya yin hakan ba tare da masarautun gargajiya ba, hakan ce tasa jihar Kano ta sami nasara,” in ji Shekarau.

Da yake bayyana nasarar kafa hukumar Hisbah a Kano, tsohon gwamnan ya ce abin da ake bukata shi ne al’umma su yadda zasu kare kansu da kansu, amma ita kuma gwamnati sai ta rika kula da su.

Ya ce hakimai da Dagatai da sauran shugabannin al’umma suna cikin wannan tsari da ake yi a Kano ba tare da wani dan siyasa ba a cikin hukumar Hisbah ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar kula da almajirai ta Kasa ta kaddamar da yiwa almajirai Rijista a Kano

Daga Saminu Ibrahim Magashi   Hukumar kula da almajirai da yaran...

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...