Daga Isa Ahmad Getso
Hukumar Hisbah ta jihar kano ta tabbatar da kama guda cikin yan matan dake yin tiktok bisa laifin yin kalaman bidala.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a cikin makwannanne hukumar ta Kama tare da gurfanar da Tauraruwar TIKTOK Murja Ibrahim Kunya bisa zarginta da aika bidala da kuma kokarin yar da hankalin al’ummar unguwar da take zaune.
Kotu A Kano Ta Yanke Wa Mutumin Da Aka Kama Da Murja Kunya Hukunci
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar a sahihin shafinta na Facebook a daren jiya alhamis.
Da dumi-dumi: Kotun Shari’ar Musulunci ta Kwace Kaddarorin Sha’aban Saboda Bashi
“Hukumar Hisbah takama Ramlat princess ta yi bidiyon da ta tallata kanta duk namijin da zai aure ta sai ya auro mata macen da za su dinga lalata da ita”. A cewar sanarwar
Zuwa yanzu dai hukumar bata bayyana Matakin da zata Dauka aka Ramlat ba, dangane da Zargin da ake yi mata Amma zamu cigaba da bibiyar lamarin.