Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta 1 da ke zamanta a GRA, Zariya, Jihar Kaduna, ta umarci Hon Sani Sha’aban, tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC, da ya biya bashin $709,238 da Naira miliyan 11.2 da Alhaji daya. Umar Faruk Abdullahi yake binsa .
Khadi, Alhaji Ishaq Madahu, a yayin da yake yanke hukuncin, ya kuma bayar da umarnin a kwace kadarorin Hon Sha’aban da aka yi amfani da su wajen yarjejeniyar bashin .
Bugu da kari, kotun ta bayar da umarnin a gaggauta nemo masu siyan kadarorin da ya bayar don warware basussukan, inda ta jaddada cewa idan darajar dukiyar da aka makala ta zarce adadin lamunin, to sai a mayar wa wanda ake kara (Sha’aban) da sauran kudinsa.
Aminu Dantata ya Bayyana Ra’ayinsa Kan Batun Sauya Tsarin Shugabanci a Nigeria
Kotun ta kuma umurci Sha’aban ya yi musu ciko idan darajar kadarorin ba ta kai adadin kuɗin da ake binsa ba.
Tattalin arziki: Tinubu Ya Gana da Gwamnoni
Daily Trust ta rawaito Lauyan wanda ya shigar da kara, Kabir Momoh, ya bayyana jin dadinsa da hukuncin, yayin da lauyan wanda ake kara, Nasir Sa’id, ya ce wanda ya ke karewa bai bashi damar yin magana da manema labarai ba akan lamarin.
Idan dai ba a manta ba a shekarar 2018 ne Honarabul Sani Mahmud Sha’aban (Dan Duran Zazzau) da Alhaji Umar Faruk Abdullahi suka rattaba hannu kan yarjejeniyar lamuni don ganin an sako shi daga wata matsala da ya samu a Dubai (UAE) a waccan shekarar.