Makarantar Haddar Alqur’ani ta Garin Lajawa Ginshiki ce na Samar da Al’umma ta Gari – Dagacin Gamarya

Date:

Daga Nura Adamu Lajawa

 

Alhaji Auwalu Dahiru Ali, Dagacin garin Gamarya dake karama hukumar Gaya ta jihar kano, ya yabawa shugabannin makarantar haddar al’qur’ani mai girma ta Lajawa bisa jajirtacewarsu wajen koyar da yaran yanke al’qur’ani mai girma.

” Babu shakka kuna da rabo mai girma a wajen Allah subhanahu wata’ala , kuma gudunnawar da kuke bayarwa wajen koyar da littafin Allah tana taimakawa wajen samar da al’umma ta gari da za ayi alfahari da ita har tashin kiyama”.

Dagacin ya bayyana hakan ne yayin bikin saukar Alqur’ani mai girma na dalubai 39 Karo na 3 a garin Lajawa, dake karamar hukumar Wudil ta jahar Kano.

Yadda Yan Sanda Suka Kama Shugabar Mata Masu Gurasa Da Suka Yi Zanga-Zanga A Kano Jami

Alhaji Auwalu Dahiru ya kuma bukaci iyayen daliban makarantar da su rika tallafawa malaman ta hanyar bibiyar karatun ya’yansu don su tabbatar suna koyar abun da ake koya musu.

Alaramma Malam Salisu Yahya shi ne shugaban makarantar kuma shi ne ya gabatar da darasi ga daliban, ya yi jawabi akan tarihin kafuwar makarantar da kuma adadin daliban da suke da su, wanda yawansu ya kai kimanin 950.

INEC ta Bayyana Sakamakon Yan Majalisun Jihar Kano Guda biyu

Malam Salisu ya kuma bayyana irin kalubale da makarantar ke fuskanta na rashin zuwan wasu daliban da wuri tare da yin fashi ba tare da wani dalili ba.

Alhaji Muhammad Jaji daya ne cikin attajiran garin Lajawa wanda ya fara qaddarar da sayan kalandar makarantar ta bana akan farashi mai daraja, tare yiwa garin na Lajawa addu’oin alkairi da samun zaman lfy.

Taron ya samu halartar manyan baki, yan siyasa, sarakuna, yan kasuwa da malaman addinin musulunci.

Malamai da dama sun yi fadakarwa tare da wa’azi da jan hankali akan matsayin Alqur’ani da irin Kariyar da Allah ya bashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...