Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Jam’iyyar APC ta kasa reshen jihar kano ta karrama guda cikin jagororinta Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso saboda gudunnawar da ya baiwa jam’iyyar tun kafin zabe da kuma bayan zaɓen shekara ta 2023 a jihar Kano.
” Kwamitin yakin neman zaben Gawuna da Garo yan takarar gwamnan kano a shekarar 2023, sune suka zauna suka ga ya dace su karrama ka saboda gudunnawar da ka bayar wajen wayar da kan yan jam’iyyar a kafafen yada labarai tun daga farkon takarar su har zuwa karshe”.
Kotun Ƙoli: Shin da gaske ne an kwalla yarjejeniya tsakanin Gwamnan Kano da Tinubu ?
Kadaura24 ta rawaito Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Gawuna da Garo Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ne ya Mika lambar yabon ga Musa Iliyasu Kwankwaso domin yaba masa kan aiyukan da ya gudanar.
” Duk Kano babu wanda ya bayar da gudunmuwar da ka bayar a kafafen yada labarai kan takarar Gawuna da Garo, hakan tasa muka ga dacewar mu karramaka don mu kara maka kwarin gwiwar cigaba da tallata manufofin jam’iyyar APC a Kano da Nigeria baki daya “. Inji Bichi
Rabi’u Sulaiman Bichi wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano ne yace akwai bukatar dukkanin jagorori da yan jam’iyyar APC na jihar kano da kasa baki daya suyi koyi da kai ” babu shakka da koya a APC irinka ne da mun sami cigaban da yafi wanda muke ciki a yanzu”.
Malam Shekarau ya yi tsokaci Kan Kiran da Ganduje ya yiwa Gwamnan Kano na Komawa APC
Da yake nasa jawabin Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya godewa kwamitin yakin neman zaben Gawuna da Garo bisa karramawar da sukai masa, sannan yace yayi abun da yayi ne domin samun nasarar yan takarar da jam’iyyar APC baki daya.
” Ina baka tabbacin zamu cigaba da kare martaba da mutuncin jam’iyyar APC a jihar Kano, saboda muna da yakinin al’ummar jihar suna kaunar yan takarar mu da jam’iyyar mu, don haka ba za mu saurara ba wajen kare martabar APC”. A cewar Kwankwaso
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun kafin zabe Musa Iliyasu Kwankwaso yake tallata manufofin jam’iyyar APC da na yan takarar ta na gwamnan kano, kuma har aka shiga kotu shi kadai ne a cikin jagororinta yake fita kafafen yada labarai don sanar da yan jam’iyyar halin da ake ciki.