Malam Shekarau ya yi tsokaci Kan Kiran da Ganduje ya yiwa Gwamnan Kano na Komawa APC

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Tsohon gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa yadda shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya kirawo gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf zuwa Jam’iyyarsu ba haka ya kamata yayi ba.

” Da ni ne da yadda dan uwana Ganduje ya nemi gwamnan Abba da Rabi’u su shiga jam’iyyar APC da ba haka zan yi ba, kamata yayi ya ce al’ummar jihar kano kowa ya zauna lafiya kowa ma yake mulki su bashi hadin kai tun da dai an rika an gama, ko ka zage su ko baka zage su ba ka ce sun iya suna dai”.

Da dumi-dumi : Kotu Ta Bayyana Dalilin Mayar da Danbilki Kwamanda Gidan Yari

Malam Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da sukai da kafar yada labarai ta DCL Hausa .

Malam Shekarau wanda tsohon Sanatan Kano ta tsakiya na yace Bai kamata a rika yin kalaman da basu dace ba akan shugabanni, Inda yace Siyasa ce shi kuma mulki lokaci ne da shi ” idan ka bar su ma shekara 4 zuwa 8 kamar yau ne zata zo ta wuce.

Dalilan da Suka sa Likitoci Suka Dakatar da Aiki a Asibitin Murtala na Kano

” Mata yayi masu mulki su daina kokarin rusa aiyukan da wadanda suka gabace suka gudanar, kamata yayi ka tsaya ka fahimci yadda abun yake sosai kafin kai ma ka fara Aiwatar da naka manufofin, domin idan aka ce za’a rika rushe aiyukan baya to babu Inda al’ummar mu zasu je”. Inji Shekarau

Sanata Shekarau ya bukaci shugabanni su daina zagin junan Inda yace yin haka shi ne yake kara rura wutar rikici da gaba a tsakanin magoya bayansu , Wanda kuma hakan ba cigaba ba ne illa koma baya da yake kawowa al’umma.

” Bai kamata shugabanni mu rika daukar lamarin Siyasar nan da gaba ba, Kamata yayi mu daina daukar wadanda ra’ayinsu ya saba da namu, a matsayin abokan gabar mu, mu Sani ba yadda za a yi kowa ya soka ko kowa ya kika, mu dauka siyasa daban mu’amala daban mu rika mutunta juna a koda yaushe hakan ne zai sa suma magoya bayanmu su yi koyi da mu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Mamallakin jaridar Nigerian Tracker ya zama Ma’ajin kungiyar masu yada labarai a kafar yanar gizo ta Arewa

Kungiyar masu yada labarai a kafafen sadarwa na zamani...

Rusau: Ana zargin an harbi mutane 6 a unguwar Rimin zakara dake Kano

Daga Nazifi Dukawa   Mazauna Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar...