Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ba ta samu sanarwa a hukumance ba game da ficewa mambobinta uku Nijar Mali da Burkina Faso ba.
Ƙasashen uku sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka karanta a gidan talabijin, inda suka zargi ƙungiyar da gazawa a taimaka musu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma matsalar tsaro.
To sai dai cikin wata sanarwar da Ƙungiyar ta fitar da maraicen ranar Lahadi, ta ce babu wata katarda da ƙasashen suka aike mata bisa wannna aniya tasu.
Ecowas ɗin ta ce tana aiki da waɗannan ƙasashen uku domin maido da su kan turbar dimokraɗiyya.
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙasashen uku na da matuƙar muhimmanci ga ƙungiyar, don haka take ƙoƙarin ganin ta lalubo hanyoyin warware matsalolin da ƙasashen ke fuskanta.