Gwamnan jihar kano ya yi wani abu da ya saba da al’ada wanda ya baiwa al’umma mamaki har suke ta magana akansa a kafafen sada Zumunta.
“Ina gajiya,naga yanda suka miki, ki yi hakuri,we will take care of it” Lokacin da Abba Kabir Yusif ya sauko yana baiwa wata mata hakuri yayin da convoy dinsa suka daki motar ta a kano.
Komai Girmanka Indai ka Shigo APC a Karkashina Zaka Zauna – Ganduje
Da yake bayyana yadda abun ya faru a fadar gwamnatin jihar kano , Gwamna Abba Kabir Yusuf yace bayan da ayarin motocinsa suka bugi motar wata mata da take tafiya a kan titi lokacin ya tsayar da ayarin motocin , Inda ya sakko domin baiwa matar hakuri.
Jarumar Hadiza Gabon Ta Yi Martani ga Masu Magana Kan Ramarta
” Bayan na tsaya wasu matasa suka taso su a tunaninsu don su na tsaya, amma haka na wuce su naje har wajen motar sai na iske wata mata ce da ‘ya’yanta a ciki, haka na bata hakurin bayan mun gaisha da ita”. Inji Abba Kabir Yusuf
” Lokacin da na Isa wajen motar sai na fahimci da ita da ‘ya’yannata duk suna cikin firgici, amma yadda muka gaisa da ita da yanyannta hakan ne yasa ta sauko ta sami nutsuwa”. A cewar Gwamna Abba Kabir
Wannan abu da gwamnan yayi ya sa al’umma na ta yi masa fatan alkhairi saboda yadda yayi abun da ba’a saba ganin irinsa ba, musamman a wajen masu mulki da Ake yi musu jiniya.