Ba zamu lamunci yadda ake yada dokokin karya na Hukumar mu ba – KAROTA

Date:

 

 

Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta karyata wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan Hukumar.

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya karyata hakan, bayan da aka kula da rubutun yana yawo a Soshiyar Midiya wanda aka yi masa suna da “SABABBIN DOKOKIN HUKUMAR KAROTA”.

Jarumar Hadiza Gabon Ta Yi Martani ga Masu Magana Kan Ramarta

Hukumar ta ce wannan rubutu da ke kunshe a cikin Soshiyar Midiya baya cikin Sabbin Dokokin da aka sabunta a shekara ta 2022 na kundin dokar da ta kafa KAROTA a shekara ta 2012.

An rantsar da Ododo a matsayin sabon gwamnan Kogi

Hukumar ta ce za ta ci gaba da kama tare da gurfanar da wadanda suke yada rubuce-rubucen karya da sunan Hukumar wajen jami’an Yan sanda.

Tuni Hukumar tare da jami’an tsaro suka dukufa wajen nemo waðanda suke yada jita-jitar tare da gurfanar da su a gaban Shari’a.

A karshe Hukumar ta ce ta kusa kammala shirinta na fassara sabuwar Dokar Hukumar da aka sabunta a shekara ta 2022 wadda za a fassarata zuwa harshen Hausa domin saukakawa jama’a fahimtar abinda ke kunshe a cikin sabuwar dokar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...