Ku dau darasi daga Buhari, ku rage buri a gwamnatin Tinubu – Garba Shehu

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bukaci al’ummar Nigeria da su rage dogon buri akan gwamnatin Bola Tinubu kada su yi wuce gona da irin kamar yadda suka yi a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari .

Da yake jawabi yayin taron tattaunawa na shekara-shekara na Daily Trust karo na 21 da Trust Media Group ta shirya a Abuja, Shehu ya bukaci ‘yan Najeriya da su rage tsammani ga shugabannin siyasa.

Gwamnan Kano Abba Kabir ya Magantu Kan Kiran da Ganduje Yayi Musu na Komawa APC

Tsohon mai magana da yawun shugaban kasar ya ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya sha fama da rikicin sa rai fiye da kima da akai masa, ina ganin darasin da ‘yan Najeriya suka koya a gwamnatin Buhari bai kamata su sake maimaita dogon buri a kan shugabannin siyasa ba .

“Dogon burin da ake sawa a gwamnatin yana yin yawa, saboda Shugabannin nan na yin abubuwa da yawa amma babu wani shugaba da zai iya yin komai.

Da dumi-dumi: Ganduje ya Gayyaci Kwankwaso, Gwamna Abba da Shekarau zuwa Jam’iyyar APC

“A zamanin Buhari, matafiya zuwa yankin Gabas su kan shafe kusan kwanaki uku a kan hanya, amma bayan gyaran hanyoyin yankin da Buhari ya yi, lokacin balaguron ya ragu zuwa kimanin sa’o’i shida.

“gwamnatin Buhari ta kuma hana shigo da shinkafa, bayan wani dan lokaci, manomanmu sun kara habbaka noman shinkafa har ma sai da takai muna iya ciyar da yammacin Afirka baki daya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...