Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa duk wani dan jam’iyyar APC a yanzu a karkashin sa yake saboda shi ne shugabanta na kasa a yanzu.
” Kada ka ji tsoro idan wani ya zo cin arziki a gidanka, shin da ka je kaci arziki a gidanka shi da ya zo yaci arziki a gidanka wanne ka fi so? , Ai mai shi shi yake da abun bayarwa, marashi shi ne mai neman wurin shiga”.
Kadaura24 ta rawaito Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da shugabannin kungiyoyin jam’iyyar APC a Ofishin Support Group dake Kano.
Gwamnan Kano Abba Kabir ya Magantu Kan Kiran da Ganduje Yayi Musu na Komawa APC
” Menene aikin shugaban jam’iyyar APC na kasa ? Aikine na jam’iyya a jihar kano kawai ? Jihohi 36 da Abuja duk inda naje nine yallabai nine alasabbanani, nine Sheikh, duk inda naje nina alangoburo, saboda haka na zaga kasar nan ina kiran gwamnoni su shigo jam’iyyar APC don mu samu karuwa, to meye laifi idan na yi haka a jihata ta kano?. Ganduje ya fada
Shugaban jam’iyyar Wanda tsohon gwamnan jihar kano ne ya ce ya sami nasarar shigo da ‘yan kananan jam’iyyu cikin har da NNPP a jihar Bauchi, “don haka a kano ma, Ina rokon yan Jam’iyyar NNPP dukkanin su da su ajiye kayan kwari su zo Inda za’a Adana musu shi a furji don kar su lalace”.
Hakikanin Yadda Siyasar Kano Zata Kasance a 2027 – Daga Bashir Hayatu Gentile
” Yanzu laifi ne Dan na kirawo yan Jam’iyyar NNPP na jihar kano su dawo APC, ai wanda yake da shi shi ake roko, wanda yake da shi shi yake bayarwa, saboda muna rokon su su auna cewa Shugabancin kasar nan a jam’iyyar zai samu?, To saboda kiransu su dawo jam’iyyar APC ai abun alfahari ne mu a wajen mu don haka mu kari muke nema, kuma kamar yadda na fada muku indai ka shigo jam’iyyar ko kai jagorane to nine shugabanka”.