Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kotun koli ta tabbatar da Kefas Agbu a matsayin zabebban Gwamnan jihar Taraba.
A zamanta na ranar Alhamis, kotun da kuma tabbatar da zaben Simi Fubara a matsayin Gwamnan Jihar Ribas.
Ina Sane Na Ki Fito Da Sakamakon WAEC Dina —Buhari
A hukunin da kwamitin alkalai biyar na kotun da Mai Shari’a Ibrahim Saulawa ya karanta, Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar gwamnan Ribas na Jam’iyyar APC, Tonye Cole, ya yi saboda rashin hujjoji.
Haka kuma, hukuncin shari’ar Gwamnan Taraba da Mai shari’a Mohammed Lawal Garba ya karanta, ya yi watsi da karar da NNPP, Yahaya Sani.
Kotun kolin ta kuma fara yanke hukunci kan daukaka karar jihar Sokkwato.