Baiwa Kananan hukumomin Hakkinsu Zai Magance Matsalolin da Dama a Nigeria – Muhd Mustapha

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

Wani Masani Dr. Muhammad Mustapha Yahaya wanda kuma shi ne shugaban kungiyar wanzar da dimokaradiyya da kawo cigaba da Magance Matsalolin tsaro Wanda akafi Sani da Action Group da dispute resolution yace baiwa Kananan hukumomi kudadensu zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro, talauci da yawan rashin aikin yi da ake fama da shi a Nigeria.

Dr. Muhammad Mustapha ya bayyana hakan ne yayin wani taro na masu ruwa da tsaki akan yadda Kananan hukumomin zasu sami yanci kasu wanda kungiyar ta shiya a shirya Masarautar Bichi.

” Rashin Adalci ne hana kananan hukumomi kudadensu, kuma hakan baya haifar da da mai ido, idan akai la’akari da tarin matsalolin da hakan ke haifarwa, don haka muke kira ga duk masu ruwa da tsaki da yi abun da ya dace don fitar da al’umma daga talaucin da aka kakaba musu”. Inji Dr. Muhammad

Cikakken Bayani da Dalilin Yadda aka Gurfanar da Danbilki Kwamanda a Kotu

Yace sun shiya taro ne domin lalubo hanyoyin da za’abi don gani Kananan hukumomin sun samin yancin cin gashin kansu daga wajen gwamnonin jihohi.

Kungiyar ta gayyaci masu ruwa da tsaki Kamar Kungiyoyi Ma’aikatar irin Kungiyar Ma’ikatan Kananan hukumomin, Mallam makarantan firemare, dagatai masu unguwani da Limamai da Sauran Kungiyoyi Mata da Matasa.

Siyasar Kano: Tinubu Ya Baiwa Kwankwaso da Ganduje Umarni

Wasu daga cikin wanda suka hallaci mahalci taro da suka hadar da Mallam Murtala Waire Wanda shine Shugaban Kungiyar Ma’ikatan Kananan hukumomin na Karamar hukumar Bichi da shugabar Kungiyar Mata Mallama Aisha sun bayana cewa baiwa kananan hukumomin yancinsu, zai taimakawa masu jama’a na kasa su fita daga kuncin rayuwar da suke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...

Yin rijistar katin Zabe zata taimaki addinin musulunci da musulmai – Mal Usman Mai Dubun Isa

Shahararren mai yabon Manzon Allah (S A W) Malam...